Katsina ta yi dokar daurin rai-da-rai ga masu fyade

Image caption Mata a Nigeria na fuskantar barazanar fyade.

Majalisar dokokin jihar Katsina ta zartar da dokar da ta tanadi daurin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da laifin fyade.

Majalisar ta zartar da dokar ne ranar Talata a wani garambawul da ta yi wa tsohuwar dokar da ke aiki a jihar wacce ta ba da zabin daurin rai-da-rai ko kuma kasa da haka ga masu fyade.

Mata a Nigeria dai na kokawa da yawan fyade da ake yi musamman ga kananan yara.

Sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin bil'adama na cewa mata da dama da aka yi wa fyade ba su cika neman hakkinsu saboda gudun tsangwama da kyama.