Shin waye zai gaji Nelson Mandela?

Image caption Gandhi da Mandela da Suu Kyi

Ana kallon Nelson Mandela a matsayin "jagora kuma uba na duniya", wanda ke kokarin warware matsalolin da ake fuskanta a kasashe daban-daban.

Kwarjininsa da gaskiyarsa ta sa mutane na kallonsa a matsayin magajin Mahatma Gandhi na India.

Amma kuma waye zai maye gurbinsa?

Nelson Mandela ya shiga tsakani a rikice-rikice a duniya irinsu na Lockerbie a Libya da Burundi da Jamhuriyar Demokradiyar Congo da Lesotho da kuma Indonesia.

Ya tsoma baki a kan rikicin Isra'ila da Palasdinawa, da na yankin Kashmir tsakanin India da Pakistan da kuma yaki da kwayar cutar HIV.

Magajin Mandela?

Image caption 'Yan kungiyar dattawa da Mandela ya kafa

Mandela na tsage gaskiya komai dacinta, abinda ya sa ake girmamashi a duk duniya.

A shekara ta 2007, ya kafa wata kungiya ta dattawa a duniya wacce za ta dinga bada shawarwari da kuma gudunmawa wajen shawokan manyan matsalolin da duniya ke fuskanta.

Wani marubuci, David James Smith ya ce irin dabi'ar Mandela ta sa da kamar yuwa a samu wani kamarsa, amma kuma ya ce 'yar siyarsa kasar Burma, Aung San Suu Kyi na da wasu hallaya irin na Mandela.

Gandhi, Mandela da kuma Suu Kyi duk sun sha dauri a kurkuku saboda sadaukar da kai don kwatowa mutanensu 'yanci, duk da cewar akwai wasu irinsu a China da Koriya ta Arewa wadanda ba a san dasu ba.

Karin bayani