Boko Haram:'An kashe mutane 1,200 cikin wata 6'

Jami'an tsaro na sintiri a jihar Borno
Bayanan hoto,

Jami'an tsaro na sintiri a jihar Borno

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe mutane fiye da dubu daya da dari biyu a rikice-rikicen dake da nasaba da masu kaifin kishin Islama daga lokacin da gwamnatin Najeriya ta saka dokar ta baci a yankin arewa maso gabashin kasar, a watan Mayu.

Majalisar ta ce adadin ya hada da kashe kashen da 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis sunnah lid'da'awati wal jihad da ake kira Boko Haram suka yi na fararen hula da sojoji a jihohin Adamawa da Borno da Yobe.

Adadin ya kuma hada da masu tada kayar bayan da sojoji suka kashe a lokacin da suke kokarin dakile harin da ake kai musu.

Wannan shi ne karon farko da wata hukuma mai zaman kanta ke fitar da adadin mutanen da aka kashe tun da aka kafa dokar ta bacin.

Har yanzu kungiyar Boko Haram na kai hare hare duk kuwa da yawan sojojin da aka tura yankin.