An kashe mutane goma a Adamawa

Image caption Jami'an tsaro na fuskantar kalubale wajen tunkarar 'yan bindiga

Rahotanni daga jihar Adamawa da ke Nijeriya na cewa mutane akalla goma ne suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata, yayin da wasu 'yan-bindiga da ake jin 'yan fashi da makami ne suka kai hari ranar Laraba da rana a wata kasuwa a garin Mubi.

Garin dai yana da nisan kimanin kilomita dari da hamsin arewa da Yola, babban birnin jihar.

Rahotannin dai na cewa 'yan bindigar sun kashe mutane biyar, yayin da su ma 'yan bindiga biyar suka rasa nasu rayukansu a yayin musayar wuta da jami'an tsaro wadanda suka kai dauki.

Maharan sun kuma kwace dukiya daga hannun 'yan kasuwa da bakin bindiga.nigeria police

Karin bayani