'Yan majalisar wakilan Nigeria sun koma APC

Image caption Jam'iyar APC dai sai dada samun magoya baya take yi

'Yan majalisar wakilan Nigeria 37 da aka zaba a karkashin jam'iyar PDP mai mulkin kasar sun koma jam'iyyar adawa ta APC.

'Yan majalisar sun bayyana sauya shekar ne a zauren majalisar ranar Laraba.

'Yan majalisar da suka sauya shekar sun fito ne daga jihohin gwamnonin nan biyar da suka koma jam'iyar ta APC a watan jiya.

Jihohin da gwamnonin suka koma su ne Kano da Adamawa da Rivers da Kwara da Sokoto.

Karin bayani