Atiku na shawarar komawa APC

Image caption Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria, Atiku Abubakar ya ce zai shawarci magoya bayansa game da komawa jam'iyyar adawa ta APC.

Atiku Abubakar ya baiyana haka ne safiyar Laraba, yayin da ya karbi bakuncin jagororin jam'iyyar da suka hada da Janar Muhammadu Buhari ritaya da Cif Bola Tinubu.

Atiku Abubakar ya taba barin jam'iyyar PDP ya koma AC inda ya yi takarar shugaban kasa sai dai daga bisani ya koma PDP.

Koda yake tun komawarsa jam'iyyar ya na cikin masu adawa da bangaren shugaba Goodluck Jonathan.