Gwamnatin Mali ta bayyana nasara a zabe

Image caption Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita

Gwamnatin Mali ta ce kawancen jam'iyyun dake goyon bayan shugaba Ibrahim Bubakar Keita sun cinye zabukan majalisar dokokin kasar.

Ma'aikatar da ta shirya zagaye na biyu na zaben a ranar Lahadi ta ce jam'iyyun dake kawance da shugaban kasar sun cinye kujeru 115 cikin kujeru 147.

Ba'a dai rigaya an tabbatar da sakamakon zaben ba.

Ana kallon zaben nan ne a matsayin wani mataki na mayar da Mali kan turbar dimockadiyya bayan juyin mulkin da aka yi cikin shekarar 2012 da kuma tsoma bakin sojojin Faransa - wadanda suka fatattaki 'yan tawaye 'yan kishin Islama daga arewacin kasar.