Niger za ta soma fitar da mai a shekarar 2016

Image caption Shugaba Mahamadou Issofou

Jamhuriyar Niger na shirin soma fitar da danyen mai zuwa kasuwanni kasa da kasa daga shekara ta 2016.

Shugaban kasar, Mahamadou Issoufou shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi a kafafen yada labarai a cikin kasar.

A cewarsa "Gwamnati ta bada umurnin a gaggauta gina bututan mai wadanda za a dinga fitar da danyen mai daga shekara ta 2016."

Dama dai Niger din ta nuna sha'awarta na soma fitar da mai zuwa kasashen waje ta wasu manyan bututan mai da za su ratsa ta kasar Chadi da Kamaru har zuwa cikin tekun Atlantic don isa kasashen Turai.

Niger na da arzikin ma'adanin Uranium kuma a shekara ta 2011 ta soma hakko danyen mai inda a kowacce rana take fitar da ganga 20,000 daga matatar ta dake Agadem a gabashin kasar.

Matatar mai ta Soraz a Niger mallakar gwamnatin kasar ce da kuma kamfanin mai na kasar China.

Karin bayani