'Galibin matasan Nigeria na zaman kashe wando'

Image caption Matasa masu yi wa Nigeria hidima

Hukumar kididdiga ta Nigeria ta bayyana cewar kashi hamsin da hudu cikin dari na matasan kasar ba su da aikin yi.

A sabon rahoton da hukumar ta fitar bisa wani bincike da ta gudanar a shekara ta 2012, kashi 48.1 cikin 100 na matasa maza na zaman kashe wando a yayinda kashi 51.9 cikin 100 na 'yan mata ba su da aikin yi.

A cewar rahoton kasar na da matasa kusan miliyan 64 wadanda shekarunsu ke tsakanin 15 zuwa 35.

Rahoton kuma ya bayyana cewar jihar Lagos ce tafi kowacce jiha yawan matasa sai kuma jihar Kano dake bi mata a yayinda a jihar Bayelsa ake da adadi mafi karanci na yawan matasa a Nigeria.

An fitar da wadannan alkalumanne a daidai lokacin da gwamnatin Nigeria karkashin jagorancin Dr Goodluck Jonathan ke cewar ta fitar da wasu shirye-shirye don samar da ayyukan yi a tsakanin matasan kasar.

Karin bayani