PDP ta zargi 'yan majalisa da cin amana

Bamanga Tukur
Image caption ' 'yan majalisar da suka sauya sheka za su fuskanci hukunci'

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya ta bayyana canza shekar da wasu 'yan majalisar dokokin kasar 37 suka yi zuwa babbar jam'iyyar adawa ta APC a matsayin wani abu na cin amana ba wai kawai ga jam'iyyar ta PDP ba, har ma da miliyoyin mutanen da suka zabe su zuwa majalisar.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP Chief Olise Metuh ya ce a matsayinsu na masu yin dokoki, babu shakka wadanda suka sauya shekar su na da masaniyar tanade-tanaden tsarin mulki, wanda ya fayyace karara sharuddan da za su sanya wani dan majalisar dokoki ya sauya sheka.

Jam'iyyar ta PDP ta yi kashedin cewa duk wani wakili na majalisar dokoki ta kasa ce ko ta jiha wanda ya balle daga hadaddiyar jam'iyyar PDP sabanin shelar da kotu ta yi cewar jam'iyyar ba ta da wasu bangarori ko rassa, to dole ne ya shirya fuskantar hukunci na sauya shekar a bisa tanade-tanaden tsarin mulkin Nigeria.

Jam'iyyar ta PDP ta yi Allah Wa dai da juyin siyasar dake faruwa cikin hanzari a matsayin wani kulli na son zuciya da wasu 'yan siyasa ke da shi na haddasa rudani a siyasar Nigeria.

A ranar Laraba ne dai wasu 'yan majalisa na jam'iyyar PDP mai mulki su 37 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC.