An kashe mutane hudu a Pilato

Image caption Fiye da shekaru 10 ana asarar rayuka a Pilato.

Wasu mahara a jihar Pilato dake arewa ta tsakiyar Nijeriya sun kashe akalla mutane hudu ciki har da kananan yara biyu sa'adda suka afkawa kauyen Heipang.

Maharun sun kuma jikkata wasu mutanen biyu a harin da suka kai daren Laraba.

Kawo yanzu dai ba a iya tantance hakikanin wadanda suka kai harin ba, amma dai wadanda lamarin ya rutsa da su yan kabilar Berom ne.

Fiye da shekaru 10 ke nan ana fama da yawan zubar da jini da ake dangantawa da kabilaci da addini da kuma siyasa a jihar ta Pilato.