Ana ci gaba da gwabza fada a Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu
Image caption An kashe daruruwan mutane a rikicin

A Sudan ta kudu ana ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawaye duk da ikirarin da gwamnati ta yi a baya cewar dukkan biranen kasar suna karkashin ikon ta.

Wani kakakin Soji ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Rueters cewa, iko da Bor babban birnin jihar Jonglei ya subuce ma gwamnatin.

Magajin garin Bor Nicholas Nhial Maja ya fada wa BBC cewar an shiga wani hali na rudami, saboda mummunan fadan da ake gwabzawa a tsakiyar birnin.

Shugaban Sudan ta Kudun Salva Kiir ya ce a shirye yake ya yi tattaunawar sulhu da abokin hamayyarsa kuma tsohon mataimakinsa Riek Marchar don kawo karshen rikicin wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan jama'a.

Mr .Kiir ya zargi Mr. Marchar da laifin yunkurin kifar da gwamnatin - zargin da Mr. Machar ya musanta.

Karin bayani