Shugaba Kiir ya yi tayin sasantawa

Image caption Tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar

Shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir ya ce, ya shiryawa tattawana da 'yan adawa da kuma tsohon mataimakinsa Mr Riek Machar domin kawo karshen tashe-tashen hankulan da kasar ke ciki na kwanaki hudu da ya yi sanadiyyar rasa rayukan daruruwan al'umar kasar.

Bukatar sasantawar ta biyo bayan kiran da sakatare janal na Majalisar dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi, inda ya bukaci Mr Kiir da ya sasanta da dukkan bangarorin ta kowacce hanya.

A nasa bangaren Mr Machar ya ce, 'yan tawayen SPLA na bukatar sauyi kuma shugaba Salva Kiir ya yi murabus;

Ya ce, "a bayyane take 'yan tawayen SPLA na danasanin shugabancin Salva Kiir, dan haka bamu da wani zabi illa mu bukace shi da yayi murabus, ya bar mulkin nan."

Mr Machar ya kuma zargin Mr Kiir da kokarin murkushe masu sukar gwamnatinsa

Karin bayani