Edwin Clark ya nemi Goodluck ya tankawa Obasanjo

Image caption Obasanjo da Goodluck lokacin suna danyen ganye.

Wani jagoran kabilar Ijaw a Nigeria, ta su shugaban kasar Goodluck Jonathan, Cif Edwin Clark ya shawarci shugaban da ya mayar da martani game da wasikar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya aika masa.

Cif Edwin Clark, wanda shi ma aka yi wa shagube a cikin wasikar ya karyata zarge-zargen da tsohon shugaba Obasanjo ya yi wa shugaba Goodluck Jonathan.

Ya kuma bukaci Mr Jonathan da ya dauki lokaci ya amsa wasikar dalla-dalla nan ba da dadewa ba.

Ya ce: "Ka amsa batutuwan da ke cikin wasikar daya bayan daya don gamsuwar 'yan Nigeria ba wai don Obasanjo ba."

Wasikar dai mai shafuka 18 ta kunshi zarge-zarge da su ka hada da batun horar da 'yan bindiga domin kashe 'yan adawa, fifita kabilar Ijaw kan sauran 'yan kasar, sabawa alkawarin wa'adin mulki guda daya da kuma wasu muhimman batutuwan da suka shafi mulki da siyasar Nigeria.