An aurar da mata fiye da 1000 a Kano

Image caption Gwamnatin Kano ta ce ta bullo da shirin ne domin rage matsalolin da suka shafi iyali.

Gwamnatin jihar Kano da ke Nigeria ta aurar da mata 1111 a karkashin tsarin auren da hukumar Hizba ta jihar ke shiryawa.

Cikin wadanda aka daura wa auren har da zawarawa da mabiya addinin Kirista da masu fama da cutar HIV.

Wannan ne dai karo na hudu da hukumar ke shirya irin wannan aure da nufin rage yawan zawarawa da kuma magance yawaitar mutuwar aure.

Gwamnatin Kano da 'yan kasuwa da kuma wasu kamfanoni ne dai ke daukar dawainiyar angwayen da amare.

Karin bayani