A yi ma hukumar tsaro ta Amurka garenbawul

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Wani Kwamiti da Shugaban Amurka Barack Obama ya kafa don ya sake tsarin yadda hukumar tsaron kasa ke tafiyar da harkokin ta na leken asiri ya ba da shawarar cewa kamata ya yi nan gaba sauraren layukan waya na wasu Shugabannin kasashe ya zamo da umurni daga sama.

Wannan yana daya daga cikin shawarwari fiye da arba'in da kwamitin ya bayar a wani rahoto mai shafi dari ukku wanda kuma ya nemi wata hukumar ta rinka sa ido ko kuma tattara bayanan wayoyin da 'yan kasar ta Amurka suka yi ko sakonni ta waya da maganganu ta yaanar-gizo, baa wai ita hukumar tsaron kasar ba.

Wani wakilin BBC a birnin Washington ya ce, wasu daga cikin shawarwarin sun gitta ma hukumar sharudda da dokoki kan yadda za ta tafiyar da ayyukan ta.

An kafa kwamitin ne bayan tsohon jami'in leken asirin nan na Amurkar Edward Snowden ya fallasa bayanan sirri na hukumar tsaron kasar.

Karin bayani