Sabon salon satar jarirai a Najeriya

wata uwa da jaririnta
Image caption Ana sayar da jariran ga wadanda ba su haihu ba ko wadanda za su yi tsafi da su

Wata sabuwar matsala ta fizge jarirai daga hannun mata masu goyo, da tserewa da jariran ta kunno kai a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Wannan al'amari dai ana ganin wani sabon salo ne na matsalar safarar jarirai da ake fama da ita galibi a yankin kudu maso gabashin kasar.

A yankin a kan killace 'yan matan da suka yi ciki shege a wasu gidaje, da ake fakewa da cewa na renon marayu ne, har 'yan matan su haihu a sayar da jariran.

Ana ganin sakamakon matakan da hukumomi ke dauka na hana sauran hanyoyin safarar jarirai ne yanzu kuma aka bullo da wannan salon.