An kashe Sojojin India a Sudan ta Kudu

Image caption Shugaba Obama ya bukaci shugabanin kasar ta Sudan da su gaggauta mai do ta kwanciyar hankali a kasar.

Jakadan India a Majalisar Dinkin Duniya, Ashok Mukerjee, ya ce an kashe sojojin kiyaye zaman lafiya uku daga kasarsa a cikin wani hari da aka kai wa sansanin Majalisar a Sudan ta Kudu.

Mr Mukerjee ya ce dakarun sun mutu ne sa'adda 'yan kabilar Nuer suka afkawa sojan majalisar a sansaninsu da ke Akobo.

'Yan kabilar Nuer masu tawaye sun kai harin ne kan fararen hula 'yan kabilar Dinka masu rinjaye, wadanda suka fake a sansanin.

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ba ta tabbatar da mutuwar sojojin ba.

Sudan ta kudu dai ta afka cikin rudani ne tun bayan da shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin yi masa juyin mulki.

Karin bayani