An bindige wani kanar din soja a Libya

Image caption Kanar Jaziri ya gadi Ahmed Barghathi ne wanda shi ma bindige shi aka yi yayin da ya ke barin gidansa domin halartar Sallar Juma'a a watan Oktoba.

An bindige sabon shugaban sashen tattara bayanan sirri na sojin Libya a gabascin kasar.

An kai wa Kanar Fathullah Aljaziri hari ne a garin Derna da ke kusa da birnin Benghazi sa'adda ya ke dawowa daga bukin auren wani dan uwansa.

An dai nada shi bisa wannan mukamin ne a cikin watannan. Masu aiko da rahotanni sun ce garin na Derna wata matattara ce ta masu tsattsauran ra'ayin addini.

'yan bindiga sun kai hare-hare masu yawan gaske kan jami'an tsaro da alkalai da makamantansu a gabascin Libya tun daga shekara ta 2011.

Karin bayani