Ba mu ci amanar PDP ba - 'Yan majalisa

Image caption PDP na kokarin dawowa da 'yan majalisarta da suka koma APC a Nigeria.

'Yan majalisar wakilan Nigeria da suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar zuwa jam'iyyar adawa ta APC sun fara mai da martani kan zargin cin amana da jam'iyyar PDPn ta yi musu.

Alhassan Ado Doguwa, dan majalisar wakilai daga jihar Kano ya shaidawa BBC cewa PDP ce ta ci amanarsu saboda karya dokokin jam'iyya, tsarin mulkin kasa, da ma tsarin dimokradiyya da ya ce shugabannin PDP na yi.

Dan majalisar ya kuma ce matakin da suka dauka na barin jam'iyyar ya zo daidai da ra'ayin wadanda suka zabe su, wadanda su kadai ne ke da damar yanke hukuncin wa ya ci amanar wani tsakaninsu da jam'iyyar.

Game da barazanar da PDP ta yi musu kuwa cewa tilas su koma jam'iyyar, Alhassan Doguwa cewa ya yi: "Bakin alkalami ba ma bushe wa yayi ba, bayan ya bushe ma bakin alkalami ya karye das. Maganar mu mu waiwaya wannan matakin da muka dauka ba zamu fasa ba."