Uganda ta haramta shigar tsiraici

Image caption Za'a kama duk wacce ta sa kayan da ba su rufe gwiwa ba.

'Yan majalisar Uganda sun zartar da dokar da za ta haramta amfani da dangalallen siket.

An zartar da dokar yaki da tsiraici na zahiri da na hotunan bidiyo ne bayan gajerar tattaunawa.

Lokacin da ministan kyautata dabi'ar al'umma Simon Lokodo ya gabatar da kudirin dokar a farkon shekarar nan ya ce za'a kama duk macen da sa tufafin da bai wuce gwiwarta ba.

Uganda kasa ce mai ra'ayin mazan jiya wacce ta ke kokarin tsananta dokar haramta luwadi da madigo, gami da hukuncin kisa ga wadanda aka samu da wannan dabi'a.

A cewar jaridar Monitor mai zaman kanta, sabuwar dokar za ta haramta duk wani tufafi da zai bayyana tsiraici ko kuma duk wata shiga mai tada sha'awa.