'A hukunta masu hannu a fadan Afrika ta Tsakiya'

Image caption Rikicin ya soma ne bayan da Michel Djotodia wanda musulmi ne ya yi wa Francois Bozize wanda kirista ne juyin mulki.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Samantha Power, ta ce ya kamata a hukunta wadanda ke da alhakin rikicin addini a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Ms Power ta bayyana hakan ne bayan da ta gana da shugaban kasar mai rikon kwarya, Michel Djotodia da sauran jagororin kasar, a babban birnin kasar Bangui, inda kuma ta ziyarci wadanda rikicin ya rutsa da su.

Jakadiyar ta Amurka ta ce irin rahotannin da ake ji na rikicin abu ne mai tada hankali matuka gaya.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce su na fargabar kusan mutane 1,000 a ka kashe a farmaki na kwana biyu da aka kai a farkon watan nan inda ake zargin tsofaffin 'yan tawaye da galibinsu Musulmi ne da ramuwar gayyar hare-haren da kungiyoyin 'yan bindiga Kiristoci suka kai.

Karin bayani