Ƙasashe za su hada kai kan harin Lockerbie

Image caption Kasashen uku sun ce suna son ganin an gano tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a lamarin a gaban kotu.

Yayin tarukan cika shekaru 25 da harin bam din da ya haddasa faduwar jirgin saman Amurka a garin Lockerbie na Scotland, hukumomin Birtaniya da Amurka da na Libya sun ce za su hada kai domin gano gaskiyar lamarin.

Kasashen sun ba da wannan sanarwa ce yayin da ake gudanar da addu'oin tunawa da mutane 270 din da suka mutu lokacin da aka tarwatsa jirgin na Pan Am mai lamba 103 a sararin samaniyar garin Lockerbie na Scotland.

An samu mutum daya, wani jami'in leken asiri na Libya Abdelbaset al-Megrahi da laifin kitsa harin amma kuma har ya zuwa lokacin da ya rasu a shekarar da ta wuce ya kafe kan cewa ba shi da hannu a lamarin.