''Da gangan aka fado da jirgin Mozambique''

Image caption Ba a san dalilin da ya sa matukin jirgin ya haddasa hadarin ba

Kwararru akan harkar sufurin jirgin sama a Mozambique sun ce matukin jirgin saman kasar da ya yi hadari a Namibia a watan da ya wuce, da gangan ya haddasa hadarin.

Mutane 33 ne suka mutu a hadarin jirgin, wanda ya rikito kasa.

Shugaban cibiyar nazarin sufurin jirgin sama ta Mozambique, ya ce matukin jirgin ya sarrafa na'urar da ke tafiyar da jirgi ba tare da matuki ya sarrafa jirgi ba, ta yadda aka gano cewa ya sarrafa na'urar ta yadda za ta haddasa faduwar jirgin da niyya.

Wannan dai sakamakon binciken farko ne yayin da ake ci gaba da gudanar da binciken.