APC ta gana da Obasanjo

Image caption Bisi Akande, shugaban riko na APC

A Najeriya shugabannin jam'iyyar adawa ta APC sun gana da tsohon shugaban kasar, Chief Olusegun Obasanjo a Abeukuta kuma Obasanjon ya ce, APC alheri ce ga fagen siyasar Najeriya.

Gwamnonin nan biyar na PDP da suka sauya sheka zuwa APC su ma sun halarci taron.

Taron dai ci gaba ne na ganawar da APC take yi da bangarori daban-daban na siyasar Nijeriya.

An ambato Obasanjo yana cewa, APC ta na kan turbar da ta dace a fagen siyasar Nijeriya.