Musulmi na zanga zanga kan sojin Faransa

musulmi masu adawa da sojin Faransa a Bangui
Image caption Rikici tsakanin musulmi da kirista ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Rahotanni daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na cewa dubban musulmi sun yi zanga zanga a babban birnin kasar Bangui domin adawa da sojojin Faransa da suke karbe makamai a hannun jama'a.

Faransa dai ta tura sojojinta 1,600 zuwa kasar a farkon watan nan domin su tallafa wa dakarun tabbatar da zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika da suke fafutukar shawo kan rikicin Musulmi da Kirista.

Masu aiko da labarai sun ce al'ummar Musulmi da ba su da yawa a birnin na Bangui, suna korafin cewa shirin karbe makaman zai jefa su cikin hadarin fuskantar harin kiristoci.

A ranar Alhamis kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, ta ce dukkkanin bangarorin da ke rikici a Afrika ta Tsakiyan sun aikata laifukan yaki, duk da kasancewar dakarun kasashen waje a kasar.