PDP ta gana da 'yan majalisar da ba su sauya sheka ba

Image caption Wannan dai shi ne karon farko da aka kwacewa jam'iyyar ta PDP rinjaye a Majalisar.

Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta yi wani taro da 'yan majalisar wakilanta a karon farko bayan da 37 daga cikinsu suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Bayanan da suka fito daga zauren taron dai sun ce Jamiyyar ta yi alkawarin bai wa 'yan Majalisar Tarayya na Jami'yyar wadanda ba su bar Jamiyyar ba tikitin takara ba hamayya a zabe mai zuwa na shekara ta 2015.

Ga alamu wannan yunkuri ne na shawo kan yadda 'yan majalisar ke ficewa daga jam'iyyar inda kawo yanzu 37 suka sauya sheka zuwa APC abinda ya sa APCn ta samu rinjaye a majalisar.

Sai dai daya daga cikin 'yan majalisar jam'iyyar da suka riga suka sauya sheka ya ce wannan matakin ba zai sa su sake waiwayar PDPn ba.

''Wallahi mun gwammace kada mu koma majalisar nan da mu kasance cikin majalisar (amma) an jefa bangarenmu, an jefa mutanenmu cikin masifa da bala'i'' inji Hon. Aminu Sulaiman Fagge dan majalisar wakillai daga jahar Kano.

Karin bayani