Sudan ta Kudu: Faɗa ya na ƙara muni

Babban jami'in kula da ayyukan jin kai na majalisar dinkin duniya a Sudan ta Kudu, Toby Lanzer ya shaidawa BBC cewa dubban mutane na cikin fargabar rasa rayukansu.

Hakan na faruwa ne yayin da fadan ƙabilanci ke ƙara muni.

Mr Lanzer ya ce da idonsa ya ga ana bindige mutane a kan tituna, yayin da wasu kuma ke ta ruguguwar shiga cikin farfajiyar ginin majalisar dinkin duniya a garin Bor.

Ofishin majalisar dinkin duniya a Sudan ta Kudu ya kuma ce, zai kwashe ma'aikatansa da ayyukansu ba su zama dole ba, daga kasar, ganin yadda rikici ke ƙara ƙazancewa.

Za a mayar da ma'aikatan ne kasar Uganda makawbciyarsu.

Karin bayani