EFCC ta gayyaci wasu jami'an gwamnatin Kano

Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso
Image caption Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Nigeria zagon kasa ta gayyaci shugaban majalisar dokokin jihar Kano tare da sauran manyan jami'an majalisar bisa binciken gyaran kasafin kudin bana.

Shugaban kamitin bin diddigin yadda ake kashe kudin gwamnati na majalisar Rabiu Sale Gwarzo wanda ba ya cikin wanda aka gayyata, ya shaida wa BBC cewa shugabannin majalisar takwas da kuma ma'aikata uku aka gaiyata.

A cewar Hon. Rabiu Gwarzo takardar gayyatar da EFCC ta aikewa majalisar ta ce gayyatar na da dangantaka da gyaran kasafin kudin da gwamnatin jihar ta nemi yan majalisar su yi a makon jiya na Naira Biliyan 28.

Sai dai manazarta na ganin hakan ba zai rasa nasaba da siyasa ba, musamman ma da gwamnan jihar Rabiu Kwankwaso ya koma jam'iyyar hamayya ta APC.