An sace wani kwara dan Lebanon a Kano

Image caption Taswirar Nigeria

Wasu 'yan bindiga a jihar Kano da ke arewacin Nigeria sun sace wani kwara dan kasar Lebanon.

Da safiyar Litinin ne maharan suka kama Mr Hassan Zain, janar manaja na kamfanin robobi na PVC, yayin da suka bude wuta a ofishinsa.

Akalla mutane biyu ne suka jikkata lokacin harin.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da lamarin, inda ya ce 'yan sanda su na bincike da nufin ceto mutumin da aka sace.

Akwai 'yan Lebanon da dama a jihar Kano da wasu jihohin Nigeria wadanda ke kasuwanci a kasar.

Karin bayani