Rashin aiki na damun matasan Afrika

Matasan Afrika
Image caption Matasan Afrika

Matasa a kasashen Afrika sun bayyana rashin aikin yi a matsayin babbar matsalar dake tarnaki ga ci gabansu.

Matasan sun bayyana hakan ne a karshen wani taron koli na matasan Afrika da aka kammala a Rwanda inda wakilai daga kasashen Afrika fiye da 30 su ka halarta.

Daya daga cikin mahalartan, shugaban majalisar matasa na kungiyar kasashen CommonWealth Ahmed Adamu ya shaidawa BBC cewa maganin matsalar shi ne horar da matasa kan kirkiro sana'o'i na kan su.

Ahmed Adamu ya kuma bukaci kasashen Afrika su rinka horar da matasa cikin harsunan da suke fahimta ba na kasashen waje ba.

Ya kuma shawarci gwamnatocin nahiyar da su ware wa matasa kujerun shugabanci domin damawa da su a harkokin siyasa.