Nijar za ta bunkasa noman rani

Image caption Manoma a Nijar.

Gwamnatin Nijar ta ce za ta bunkasa noman rani a bana domin cike gibin amfanin da aka samu a noman damuna.

Ministan kasa a ministar ayyukan noma Alhaji Abdu Labbo ne ya baiyana haka bayan gudanar da rangadi a jihar Damagaram.

Alhaji Abdu Labbo ya ce an yi rashin ton 50,000 a jihar Damagaram yayin da a fadin kasar kuma aka samu rashin ton 343,000.

Sai dai ya ce noman ranin da za'a yi bana zai samar da ton 400,000 abinda zai cike gibin da aka samu a damuna.

Haka kuma ministan ya ce an samu gibin ton miliyan 6.8 na abincin dabbobi amma gwamnatin ta ware CFA miliyar 6.7 domin samar da abincin da kuma kula da lafiyar dabbobin.