'Za mu kare Amurkawa a Sudan ta Kudu'

Image caption wani Jami'in agajin ya ce yanayin da ake ciki a Sudan ta Kudun zai kara muni a kwanakin da ke tafe in har ba a kawo karshen fadan ba.

Shugaba Barack Obama ya ce Amurka na iya daukar karin mataki a Sudan ta Kudu idan har hakan ya zama wajibi, domin kare Amurkawa da kuma ofishin jakadancin kasar da ke can.

A ranar Asabar ne aka raunata wasu sojin Amurkan hudu lokacin da aka harbi jirginsu yayin da suke kokarin kwashe Amurkawan daga garin Bor.

Yanzu dai ma'aikatar harkokikn wajen Amurkar ta ce an kammala aikin kwashe 'yan kasar daga Sudan ta Kudu wadda ta tsunduma cikin yakin basasa, a cikin nasara.

Gwamnatin Britaniya ma za ta aike da jirgi na karshe domin kwashe ragowar 'yan kasarta daga Juba.

Karin bayani