Rikici na kazanta a Sudan ta kudu

Image caption Dubban mutane sun bar gidajensu a Sudan ta kudu

Ana ci gaba da gwabza fada a Sudan ta kudu inda ake kashe kashe na kabilanci.

Rikici tsakanin dakarun da suke biyayya ga Shugaban kasar Salva Kirr wanda dan kabilar Dinka ne da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar dan kabilar Nuer ya watsu sassa da yawa na kasar, inda kabilun biyu ke kashe junansu.

Amma Gwamnatin Sudan ta kudu ta musanta cewa tana marawa rikicin kabilanci baya.

Yanzu haka dai Majalisar Dinkin Duniya na kokarin kara tura dakarun wanzar da zaman lafiya don kare fararan hula.

Karin bayani