Dakarun Sudan ta Kudu za su kwato Bor

Image caption Farar hula da dama sun jikkata a rikicin Bor.

Dakarun da ke biyayya ga shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir na shirin kai hari kan garin Bor, wanda sojojin da ke goyon bayan tsohon mataimakinsa Riek Machar su ka kwace.

Shugaba Kiir ya ce an jinkirta kai harin ne domin ba da damar kwashe 'yan kasashen waje.

Wani da ya ke daura da Bor ya shaida wa BBC cewa mutane sun shiga cikin rudani a lokacin da su ke kokarin gujewa yakin.

Ministan hulda da kasashen waje na Sudan ta Kudu, Barnaba Benjamin ya musanta cewa dakarun soji na komawa bayan 'yan tawayen.

Ya shaida wa BBC cewa har yanzu gwamnati ce ke iko da rundunar sojin kasar.