Allurar rigakafi ta kashe jarirai a China

Image caption Kasar China ba ta sakaci da yi wa jarirai rigakafi.

Kwararrun kiwon lafiya a China na binciken mutuwar jarirai da dama wadanda aka yi wa rigakafin ciwon hanta samfurin Hepatitis B a wani shirin rigakafi na gwamnati.

Kafar yadan labaran gwamnati ta ce an tura masu bincike zuwa kamfanin da ya samar da magungunan rigakafin a garin Shenzhen dake kudancin China.

Jariran sun mutu cikin makonnin baya bayan nan, bayan da aka yi musu allurar rigakafin.