Isra'ila ta kai hare-hare a Gaza

Sojojin Isra'ila
Image caption Isra'ila ta ce ta kai hari ne a kan wuraren ta'addanci

Dakarun Isra'ila sun kai hare-hare kan zirin Gaza ta sama da kasa inda suka kashe wata yarinya 'yar shekaru uku tare da jikkata mutane goma.

Rundinar sojin Isra'ilar dai ta ce wannan mataki yana a matsayin maida martani ne ga harbe wani farar hula dan Isra'ila da aka yi kusa da kan iyaka.

Isra'ila ta ce sojan nata sun kai hari ne kan abin da ta kira wuraren ta'addanci.

Wadannan su ne hare-hare mafiya muni tun cikin watan Nuwamban bara a lokacin da Isra'ila da kungiyar Hamas suka gwabza fada na kwanaki takwas.

Wata 'yarjejeniyar tsagaita wuta ce ake aiki da ita tun lokacin, sai dai wani jami'in Hamas ya yi barazanar cewa Isra'ila za ta dandana kudarta kan wadannan hare-hare da ta kai a Gaza.

Karin bayani