Ana zargin kisan kiyashi a Sudan ta Kudu

Image caption 'Yan bindiga na bin gida-gida su na kashe wadanda ba 'yan kabilarsu ba a Sudan ta Kudu.

Rahotanni daga Juba, babban birnin Sudan ta Kudu sun ce dakarun gwamnati sun kashe fiye da 'yan kabilar Nuer 200 bayan da suka tasa keyarsu zuwa wani caji ofis na 'yan sanda.

Haka kuma a wasu unguwannin birnin, 'yan bindiga na bi gida-gida su na kashe duk wanda ba dan kabilar Dinka ba ne.

Kimanin farar hula 45,000 suka fake a sansanonin Majalisar Dinkin Duniya da ke fadin kasar, yayin da fiye da mutane 80,000 su ka kauracewa gidajensu.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya bukaci karin dakarun kiyaye zamna lafiya zuwa 12,000.