Kwankwaso ya zargi EFCC da siyasa

Rabiu Musa Kwankwaso
Image caption Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bar jam'iyyar PDP mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Gwamnatin Kano da ke arewacin Nigeria ta ce siyasa ce ta sa hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa ta kama wasu jami'an majalisar dokokin jihar, abin da hukumar ta musanta.

Gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce kama manyan jami'an majalisar da EFCC ta yi a abin takaici ne kuma koma baya ga dimokradiyyar kasar.

Ya ce an kama su ne domin cin mutuncinsu sakamakon komawarsu jam'iyyar adawa ta APC daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

Sai dai hukumar ta EFCC ta musanta wannan zargi, inda ta ce ta gayyaci jami'an majalisar ne zuwa Abuja, babban birnin kasar bayan da wani babban mutum a Kano ya zargi 'yan majalisar da saba wa dokar kasafin kudi.

Hukumar ta EFCC dai ta yi awon gaba da shugabanni da manyan ma'aikatan majalisar jihar Kano ne ranar Litinin.