Dasa bom ya ja dage shari'ar Musharraf

Image caption Pervez Musharraf zai iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai.

An dage zaman shari'ar cin amanar kasa ta tsohon shugaban kasar Pakistan, Pervez Musharraf bayan da aka samu wani bom a hanyarsa ta zuwa kotu.

Ana fuskantar Janar Musharraf ne game da matakin da ya dauka a 2007 na dakatar da kundin tsarin mulkin kasar da kafa dokar-ta-baci.

Kotun da ke Islamabad ta ce za ta ci gaba da sauraron shari'ar ranar 1 ga Janairu.

Janar Musharraf mai shekaru 70, ya musanta zargin, inda ya ce siyasa ce ta sa ake tuhumarsa.

Idan an same shi da laifi zai iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai.