Za'a yanke wa Musharraf hukunci

Parvez Musharraf
Image caption Parvez Musharraf

Lokaci ya yi da za'a yanke wa tsohon shugaban kasar Pakistan Parvez Musharraf hukunci akan tuhumar da ake masa ta cin amanar kasa sakamakon matakin da ya dauka a shekarar 2007 na dakatar da kundun tsarin mulkin kasar tare da kafa dokar ta baci.

Idan har kotun musamman a Islamabad ta kama shi da laifin, Zai iya fuskantar hukuncin kisa ko kuma na daurin rai da rai a gidan kaso.

Janar Musharraf wanda ke da kimanin shekaru saba'in da haihuwa ya musanta zarge-zargen da ake masa, inda ya ce sharrin siyasa ne kawai.

Wannan ne dai karon farko da wani tsohon shugaban mulkin soja a Pakisatan ke fuskantar tuhuma akan cin amanar kasa.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba