Bom ya kashe mutane uku a Pakistan

Image caption 'Yan Shia na kammala makokin kashe Imam Hussein fiye da shekaru 1000 da suka wuce.

Akalla mutane uku ne suka mutu sanadiyyar fashewar wani abu a garin Karachi na kudancin Pakistan ranar Talata, wacce 'yan Shia a fadin kasar ke gudanar da wasu ayyukan ibada.

Mutane kusan 10 ne kuma suka jikkata a fashewar da ta afku kafin 'yan shiar su fara jeri gwano.

An dai zuba dubunnan 'yan sanda da sojoji a kan hanyar da 'yan shiar ke bi.

An kuma haramta goyo a babur a Karachi domin maganin 'yan-harbi-ka-tsere.

Haka kuma an toshe layukan wayoyin salula a birane dabam-daban na Pakistan.