An gano makeken kabari a Sudan ta Kudu

Image caption Dubban mutane sun bar muhallansu

Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya gano wani makeken kabari da aka binne kimanin mutane saba'in da biyar a ciki a Sudan ta Kudu.

Mai magana da yawun hukumar, Ravina Shandasani ta ce akwai kabari daya wanda aka tsinci mutane 14 a ciki a garin Bentiu na jihar Unity sannan kuma an gano wasu karin kaburburan a kusa da rafi.

Garin Bentiu na hannun mayakan dake biyayya da tsohon mataimakin shugaban kasar,Riek Machar.

Tun da farko, Majalisar ta bukaci tura karin dubban dakarun wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, domin taimakawa wajen kare fararen hula da rikicin kasar ya rutsa da su.

Jakadan Faransa a Majalisar Jeeraa Arroo ya ce duka mambobin kwamitin tsaron suna da kwarin gwiwa game da ayyukan da dakarun za su gudanar a Sudan ta Kudun.

Karin bayani