Barakar APC na fadada a Sokoto

Aliyu Wamakko
Image caption Rikici tsakanin gwamnan Sokoto Aliyu Wamakko da wanda ya gada Attahiru Bafarawa na kazanta a jam'iyyar APC.

Barakar da ta kunno kai a Jam'iyar APC reshen jihar Sokoto inda yanzu jam'iyyar ke da ofisoshin jiha guda uku, sai kara fadada take yi.

Bangaren da ke tare da gwamnan jihar ya zargi bangaren da ke goyon bayan tsohon gwamna Attahiru Bafarawa da yiwa jam'iyyar PDP mai mulki aikin raba kan jam'iyyar.

Sai dai bangaren tsohon gwamnan Attahiru Bafarawa ya musanta zargin da bangaren gwamna Magatakarda Wamakko ke masa.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba