An kama tsohon Pirai ministan Masar

Image caption Hisham Firaminista ne a karkashin gwamnatin Morsi

Kafar talabijin ta Masar ta rawaito cewa, an kama tsohon Pirai minista Hisham Kandil a lokacin da yake kokarin tserewa zuwa Sudan.

Mr Kandil ya yi aiki ne a karkashin gwamnatin hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi.

Hukumomin kasar na neman sa ruwa a jallo domin ya yi zaman gidan kaso na tsawon shekara guda.

Tun da farko, wani harin bam din mota da aka kai a birnin Mansoura ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane akalla 13.

Al'ummar yankin dai sun zargi kungiyar 'yan uwa musulmi da kai harin, sai dai kuma kungiyar Ansar Beit al- makdis da ke tsibirin Sinai ta dau alhakin kai harin.

Karin bayani