An nemi Masar ta saki masu fafutuka

Image caption An daure Ahmed Maher, Ahmed Douma da Muhammad Adel saboda shirya zanga-zangar goyon bayan dimokradiyya.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Masar ta sako wasu fitattun masu fafutuka da aka daure ranar Lahadi saboda shirya zanga-zangar goyon bayan dimokradiyya.

An ruwaito kakakin ofishin kare hakkin bil'adama na majalisar na cewa bai kamata shiga zanga-zangar lumana da sukar gwamnati su zamo dalilan tsare mutane ko kuma tuhumarsu ba.

Sakatare Jananar na majalisar ma, Ban Ki-Moon ya bayyana damuwarsa, inda ya ce daure mutanen ya sabawa manufar juyin juya halin kasar Masar.