An yi mummunar ambaliyar ruwa a Brazil

Image caption Wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Brazil za su sami tallafi

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta yi alkawarin bada miliyoyin daloli tallafi ga wadanda ambaliyar ruwan da akayi kamar da bakin kwarya ta shafa.

Wannan lamari dai ya sanya rushewar gadoji da hanyoyi a jihohin Minas Gerais da kuma Espirito Santo tare da barin wasu birane ba wutar lantarki da ruwan sha.

Ms Rousseff ta kai ziyara wuraren da wannan annoba ta shafa inda ta ce ba ta taba ganin ambaliyar ruwa irin wannan ba.

Shi kuwa Gwamnan Espirito Santo Renato Casagrande cewa ya yi wannan lamari ya kazanta matuka kuma bai taba ganin irin sa a tsawon shekaru casa'in ba.

Karin bayani