An kara tura dubban sojoji Sudan ta kudu

Image caption an kara sojoji a Sudan ta kudu don kawo zaman lafiya

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura dubban sojojin wanzar da zaman lafiya da kuma 'yan sanda zuwa Sudan ta kudu don kare fararen hula daga rikicin kabilancin da ke yaduwa a fadin kasar.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce ta na fargabar cewa an kashe dubban mutane tun lokacin da aka fara rikicin makon da ya gabata.

Wani bincike da majalisar ta yi ya gano wani wawakeken rami da aka binne mutane sakamakon rikicin kabilancin a garuruwan Juba da Bentiu inda 'yan tawayen suka mamaye.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bukaci shugabannin bangarorin da ke rikicin da su fara tattaunawar sulhu, ya kuma yi kira da a gaggauta tsagaita wuta domin bawa jami'an agaji damar kai kayan tallafi a wuraren da rikicin ya shafa.

Karin bayani