Kiristoci sun kashe dakarun Chad a CAR

Image caption Dakarun Faransa da na kasashen Afrika na aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Akalla dakarun kiyaye lafiya 'yan kasar Chad guda shida aka kashe a wata arangama a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasashen Afrika ya ce 'yan bindiga masu kishin addinin Kirista na kungiyar anti-Balaka ne su ka kashe su.

Kiristocin na yaki da 'yan kungiyar Seleka wacce mafi yawansu Musulmi ne, bayan da ta kwace mulki a watan Maris.

Dubunnan daruruwan mutane ne suka kauracewa yakin inda suka fake a sansanonin sojin Faransa da na kungiyar kasashen Afrika.