Masar ta ce 'Yan uwa Musulmi 'Yan ta'adda ne

Image caption Masar ta ayyana 'yan uwa musulmi a matsayin 'yan taadda

Gwamnatin rikon kwaryar da ke samun goyon bayan soji a Masar ta ayyana kungiyar 'yan uwa musulmi a matsayin wata kungiyar 'yan ta'adda.

Wannan mataki dai zai bai wa gwamnatin damar kwace kadarorin kungiyar.

An dai zargi kungiyar ta 'yan uwa musulmi da harin da aka kai kan shalkwatar 'yan sanda ranar Talata a birnin Mansoura da ke arewacin kasar.

Harin ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 16.

Karin bayani